FALALAR BIN IYAYE //007//
Akwai ayoyi a cikin Alƙur'ani mai girma waɗanda suke nuna mana haɗuwar ibadah wadda babu damu ayi amfani da ɗaya a bar ɗaya, kamar yadda Allah (S.W.T) ya ce a cikin suratul Baƙra:-
"Ku tsaida sallah ku bada zakkah"
Suratul Baƙra, Ayah ta: 43.
A Nan tsai da Sallah da bada zakkah rukunai ne, biyu cikin rukunan musulunci da aka gina musuluncin a kai, saboda haka babu dama kace kana da imani , zakayi sallah amma bazaka bada zakkah ba, bayan kuwa kana da hali. Kamar yadda aiki mai kyau ba zai karɓu ba sai da imani, aiki mai kyau yana sanya yardar Allah. Allah (S.W.T) Ya ce:-
"Waɗanda suka yi imani suka yi aiki mai kyau za mu shigar da su cikin mutanan kirki".
Suratul Ankabut, Ayah ta: 9.
Ga kuma wani Hadisi mai kama da wannan daga babban sahabi;
An ruwaito daga Ɗan Abbas (R.A) yace:- Ayoyi uku suka haɗe da Abu uku, Ɗaya ba za ta karɓu ba sai da ƴar uwarta. Faɗin Allah (S.W.T) "ku yi biyayya ga Allah ku yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W), duk wanda yai biyayya ga Allah bai yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W) ba, ba za'a karɓa ba. Na biyu ku tsaida sallah ku bada zakkah, wanda yai sallah bai ba da zakkah ba ba za'a karɓi sallarsa ba. Na uku faɗin Allah (S.W.T) Ka gode min da iyayenka, wanda ya godewa Allah bai godewa iyayensa ba, ba za'a karɓa ba". "KITABUL-KABA'IR"
Mu haɗu a rubutu na gaba!
Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.
Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano

FALALAR BIN IYAYE //008//
Bin iyaye tare da kyautata musu ba sabon abu ba ne, tun kafin bayyanar Annabi Muhammad (S.A.W) ake horan al'ummomi da biyayya ga iyayensu har zuwa zamanin Manzon Allah (S.A.W), Kamar yadda Allah (S.W.T) Ya ce:-
"Yayin da muka riƙi alƙawari ga bani Isra'ila cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah kuma ku kyautata wa iyayenku ku zama ma su biyayya a garesu".
Suratul Baƙra, Ayah: 83.
Wani alƙawari da bani Isra'ila suka yanka wa kansu suka gabatar da shi gaban Allah (S.W.T) cewa zasu bauta masa ba za su yi tarayya da shi ba, kuma zasu zama masu biyayya ga iyayensu, ba za su yi jayyaya da falalar iyayensu ba, kuma zasu yi alƙawari ga makusantansu kuma zasu kyautatawa marayu da talakawa. Sai suka warware alƙawarin sai Allah yayi fushi dasu.
Duk ɗan kirki mai biyayya ga iyayensa zai so ya ji yadda Allah (S.W.T) ya yabi manyan Annabawansa saboda biyayya ga iyayensu tare da cewa zaɓaɓɓunsa ne a cikin hallittarsa amma saboda muhimmancin kyautatawa iyayen, Allah ya yabesu. Domin jin wannan yabo ku tara a rubutu na gaba.

FALALAR BIN IYAYE //009//
Karanta ayoyin Allah (S.W.T) da ya yabi Annabi Yahaya Amincin Allah ya ƙara tabbata a gareshi, inda yake kyautatawa iyayensa, tare da manyanta da suka yi, bai bar su ba duk kuwa da matsayinsa a wajen Allah. Allah (S.W.T) Ya ce:-
"Annabi Yahaya mai biyayya ne ga iyayensa bai zama mai girman kai mai saɓo ba".
Suratuh: Maryam, Ayah: 14.
A nan nake so na ja hankalin mai karatu, mu duba yadda Allah (S.W.T) ya fara yabon Annabi yahaya a kan bin iyayensa. Haka ma Annabi Isa Amincin Allah ya ƙara tabbata a gare shi, cikin baiwar da Allah ya yi masa ya ce:-
"Mai biyayya ne ni ga mahaifiyata, bai sanyani mai fita daga horonsa ba".
Suratuh: Maryam, Ayah: 32.
Haka yaran kirki masu biyayya za su so su ji yadda Allah (S.W.T) ya yi baiwa ta ɗa mai albarka ga Annabi Ibrahim, Amincin Allah ya tabbata a gareshi. Duk yaran kirki mai biyayya zai yi murna da yadda Annabi Isma'il ya yi, kamar yadda Allah (S.W.T) ya bayyana, Ya ce;-
Annabi Ibrahim Ya ce;- "Ya ɗana ni na gani cikin barci ina yanka ka, sai ka duba mai ka gani? sai nan da nan Annabi Isma'il ya amsa wa mahaifinsa ya ce:- "Ya Babana aikata abinda aka hore ka, za ka same ni in Allah ya so daga masu haƙuri".
Surah: Safat, Ayah; 102.
Allahu Akbar, kun ji ɗa mai biyayya. Uba ne fa ya ce zai yanka ɗansa, ɗan ya ce yanka ni Baba!

FALALAR BIN IYAYE //010//
Ina ƴaƴa masu zagin iyayensu, wani ya doki ubansa, wani kuma ya mari ubansa kowanne ɗa ya sani cewa shi fa dashen iyayensa ne kamar yadda mutane suke shuka, in ta girma su yi amfani da ita, haka ma ya kamata kowanne ɗa yayi: ya zama mai biyayya da ladabi da girmama iyayensa, domin sune sababin zuwansa duniya, su suka ɗauki nauyin rayuwarsa, tarbiyarsa, tun yana ciki har Allah ya kawo shi duniya ya rayu ya zama mutum. To a nan inde yana so ya zama me albarka yaya ze yiwa ubansa tsawa, ko ya tozarta shi cikin jama'a, balle a ce ya hana iyayensa abinci, amma ya baiwa matarsa, iyayensa ne fa suka ciyar dashi suka shayar dashi suka bashi sutura har ya girma, su kuma suka fara tsufa suna buƙatar taimakonsa a wannan lokaci, amma abin ya faskara.
DUK ABINDA IYAYE SUKA ƊAUKA CIKIN DUKIYAR ƊANSU YAYI DAI-DAI.
Allah (S.W.T) ya halatta wa iyaye dukiyar ƴaƴansu, Aisha Allah ya ƙara mata yarda ta rawaito da Annabi (S.A.W) ya ce:- "Haƙiƙa mafi daɗin abinda kuka ci daga nemanku, kuma lallai ƴaƴanku daga nemanku suke". Wato komai iyaye sukayi da dukiyar ƴaƴansu dai-dai ne domin daga garesu ya fito; su suka shuka shi har ya fito. Saboda haka babu mai hana iyaye kayan ɗansu. shi yasa imamu Ahmad da Hakim suka rawaito cewa:- "Ɗan Mutum yana daga abin nemansa, ku ci daga dukiyoyinsu kuna masu kwanciyar hankali da farin ciki".

FALALAR BIN IYAYE //011//
KA NEMI YARDAR IYAYE DAN KA SAMI YARDAR ALLAH.
Allah (S.W.T) Ya wajabta a kan ɗa da ya ciyar da iyayensa, don su ɗanɗani zaƙin wahalar da suka yi, kuma ya sa al'amarin ga iyayen daidai samari ne, ko tsofaffi ne, masu hali ne ko talakawa ne. Game da ciyarwa ya ce:-
Daga Ɗan Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya ce:- "Babu daga musulmi da yake da iyaye biyu musulmi, ya wayi gari yana mai nema masu abin da zasu ci har sai Allah ya buɗe masa ƙofofi biyu na Aljannah. In ko Uba ne kawai ko Uwa kawai ƙofa ɗaya in kuma Uba ya yi fushi da shi ko Uwa tayi fushi dashi, Allaj ba zai yarda dashi ba, har sai iyayen sun yarda dashi, sai aka ce ko su iyayen ne suka cuceshi, sai aka ce, ko sun cuceshi!".
A nan nake jan hankalinmu, mu masu iyaye da muke cikin hatsari Allah ne zai fiddamu; amma fa sai mun bi iyaye. Wannan hadisi yana nuna mana yadda aka hori ɗa da ya fita ko ina ne ya nemo abin da zai ciyar da iyayensa komai wahala. Allah zai yi masa tukwicin Aljannah, kuma ya yarda da shi, ɓatawa iyaye rai kuma yana wajabta fushin Allah da toshe rahamarsa, komai matsayin ɗan.

FALALAR BIN IYAYE //012//
SHARUƊAN BIN IYAYE GUDA UKU.
1. Lallai ɗa ya zaɓi yardar iyayensa a bisa abin da shi yake so, a kansa da matarsa da ƴaƴansa da mutane baki ɗaya.
2. Ya bisu cikin duk abin da suka hore shi, suka kuma hane shi, wannan abin ya dace da son zuciyarsa, ko ya sabawa son kansa, matuƙar basu horeshi da saɓon Allah ba.
3. Ya gabatar musu da duk abin da suke buƙata tun kafin su tambaya cikin daɗin rai da murna, kuma ya dinga gani bai yi musu komai ba ko da kuwa zai ba su jininsa da dukiyarsa.

FALALAR BIN IYAYE //013//
BI IYAYE KA SAMI YARDAR ALLAH.
Allah (S.W.T) ya gabatar da yardar iyaye kafin tasa yardar saboda matsayinsu, ya ya kuma ke nan ga mai cewa ubansa "tsohon banza!?" karanta wannan Hadisi:- [An Ruwaito haƙiƙa Allah (S.W.T) Ya aiko wajen Annabi Muaa Allah ya ƙara masa yarda, ya ce:- "Ya Musa haƙiƙa wanda ya bi iyayensa, ya saɓeni zan rubuta shi mai biyayya, wanda ya bini ya saɓa wa iyaye zan rubuta shi mai saɓawa iyaye!". ALLAHU AKBAR.
Jama'ar Musulmi mu duba inda Allah (S.W.T) Ya sanya ɗa ya yi ɗamara don neman yardar iyayensa. a kullum zuciyar mumini tana ƙoƙarin sanin abin da Allah (S.W.T) Ya ke so da kuma wanda ya yi hani don ya bi shi kuma ya kauce wa abin da ba ya so, karanta wannan Hadisi:-
Ibn Maja ya fitar a cikin littafinsa daga Jabiru Allah ya ƙara masa yarda, Haƙiƙa wani mutum ya ce ya Manzon Allah (S.A.W) ina da dukiya da ɗa, kuma haƙiƙa mahaifina yana so ya mamaye dukiya ta sai Annabi ya ce kai da dukiyar ka duk na Babanka ne. wannan yana nunawa matsayin iyaye duk halin da ɗa yake ciki Iyayensa sune sama da shi.

FALALAR BIN IYAYE //014//
KYAUTATAWA IYAYE YANA YAYE BAƘIN CIKI.
Karanta wannan Hadisi wanda Annabi (S.A.W) yake bada labari, kaga bin iyaye yana yaye baƙin ciki:-
Manzon Allah (S.A.W) yace: "Wasu mutane su uku suna cikin tafiya sai ruwan sama ya samesu, sai suka karkata zuwa kogo cikin dutse sai wani dunƙulen dutse ya toshe bakin kogon da suka shiga sai suka ce a junansu ku duba wasu ayyuka da kuka yi saboda Allah kyawawa, ku roƙi Allah da su ko Allah zai yayeta.
A - Sai na Farkonsu yace, Allah na kasance ina da iyaye biyu, sai na tatso nono kamar yadda na saba, na zo da nonon sai na tsaya nan a kansu ina mai kin na tashesu (wato sun yi barci), kuma ina ƙin baiwa ƴaƴana kafin su kuma suna ta kuka, nan ga ƙafata ban gushe ba a halin haka da su har Alfijir ya ɓulo. sai yace: Allah in kasan na aikata wannan ne don neman yardarka ka yaye mana wata ƙofa muga sama. sai Allah (S.W.T) ya yaye wata ƙofa suka ga sama.
B - Sai na Biyu yace: Ya Allah na kasance ni da ɗan uwan babana, wato ƴan maza ke son mata, sai na nemeta (da fasiƙanci) sai taƙi, akan har sai na bata dinare Ɗari. sai nai ta nema, har saida na tara dinare ɗarin, na gamu da ita. Yayin da na gurfana a tsakanin ƙafafunta, sai tace ya bawan Allah kadda ku haɗu gobe. sai na tashi. Allah in kasan na aikata haka don neman yardarka ka yaye mana wata ƙofa. sai Allah ya yaye musu wata ƙofa. AYI HAƘURI NA UKUN MU HAƊU A RUBUTU NA 15.
Mawallafi: Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.
Rubutawa; ✍️

FALALAR BIN IYAYE //015//
C - Sai na uku kuma yace, Ubangiji ni na ɗauki lebura yana raba shinkafa (wato a gona yana yi masa aiki) bayan ya gama aikinsa sai yace bani ladana. sai na kau da kai ga abrin haƙƙinsa ina shuka da abinda ya barmin na haƙƙinsa: har sai da na tara shanu da mai kiwonsu (wato haƙƙin wannan lebura da be karɓa ba, ina juyasu har ya zama dukiya) sai ya zo min can wani lokaci yace min kaji tsoron Allah kadda ka cuceni ka bani haƙƙina. sai nace masa tafi wajen saniyar can da mai kiwonta. sai yace kaji tsoron Allah kadda kayi min isgili. sai na ce ai bazan yi maka isgili ba. Ka kora shanun nan da mai kiwon, sai ya kama ya tafi. To Ubangiji idan nayi wannan ne saboda kai ka yaye sauran abinda yayi saura. Sai Allah ya yaye musu suka fito.
Allahu Akbar! jama'a ku lura da wannan hadisi mai albarka ayi taka tsan tsan da saɓawa iyaye don gudun fushin ALLAH.
Mu haɗu a rubutu na gaba!
Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.
Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano
C - Sai na uku kuma yace, Ubangiji ni na ɗauki lebura yana raba shinkafa (wato a gona yana yi masa aiki) bayan ya gama aikinsa sai yace bani ladana. sai na kau da kai ga abrin haƙƙinsa ina shuka da abinda ya barmin na haƙƙinsa: har sai da na tara shanu da mai kiwonsu (wato haƙƙin wannan lebura da be karɓa ba, ina juyasu har ya zama dukiya) sai ya zo min can wani lokaci yace min kaji tsoron Allah kadda ka cuceni ka bani haƙƙina. sai nace masa tafi wajen saniyar can da mai kiwonta. sai yace kaji tsoron Allah kadda kayi min isgili. sai na ce ai bazan yi maka isgili ba. Ka kora shanun nan da mai kiwon, sai ya kama ya tafi. To Ubangiji idan nayi wannan ne saboda kai ka yaye sauran abinda yayi saura. Sai Allah ya yaye musu suka fito.
Allahu Akbar! jama'a ku lura da wannan hadisi mai albarka ayi taka tsan tsan da saɓawa iyaye don gudun fushin ALLAH.
Mu haɗu a rubutu na gaba!
Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.
Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano
FALALAR BIN IYAYE //016//
BI IYAYE KA SAMI ALJANNAH TARE DA TSAWAN RAI DA LADAN AIKI.
An karɓo daga Abi-Ummata Allah ya ƙara masa yarda. Haƙiƙa wani mutum ya ce ya Manzon Allah (S.A.W), Menene haƙƙin iyaye akan ɗansu? sai Manzon Allah (S.A.W) Ya ce: "Su Aljannarka ce da wutarka". Allahu Akbar. Wato idan ka kyautata musu Aljannah ce makomarka in ka saɓa musu jahannama ce makomarka. hakama yazo acikin Hadisi ingantacce kamar yadda aka ruwaito;
An karɓo daga Rafi'in ɗan mukaisin Allah ya yarda da su, yana daga wanda yayi yaƙin Hudaibiyya. haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) Ya ce; "Bin iyaye yana ƙara tsawon rai, kuma sadaka tana hana mummunar mutuwa". Mai karatu na horeka da bin iyayenka tare da kyautata musu suna da rai ko bayan sun mutu, matsalar iyaye fa ba ƙaramar aba bace domin sau dayawa muna sakaci.
Karanta wannan tambayar da aka yiwa Manzon Allah (S.A.W). An karɓo daga Abdullahi ɗan Masa'udin Allah ya yarda dashi. ya ce: Na ce ya Manzon Allah (S.A.W) Wanne aikine mafifici? sai ya ce; "Sallah a kan lokacinta" sai na ce sannan me kuma? sai ya ce; "Bin iyaye" sai na ce sannan me? sai ya ce: "Yaƙi don tsaida Addinin Allah". Haka ya faɗamin, kuma da na ƙara tambayarsa don ya ƙaramin haka ya ƙaramin.

FALALAR BIN IYAYE //017//
Ina ƴaƴa masu albarka kadda ku dinga saɓawa iyayenku da abinda ze baƙanta musu rai ba bisa haƙƙi na shari'a ba, wani mugun hali da ƴaƴa suke: takun saƙa da iyayensu. Musanman a yanzu shine rashin shawara da iyaye ta yin komai kai tsaye babu neman yardarsu kamar yin tafiya ko aure da ɗaukar bashi.Ko yin hulɗa da wasu mutane kawwai dan matashi ya ga ubansa talaka ne. bashi da wata buƙata a gurinsa dan yana ganin yayi kuɗi.
Wani in har yaga mace yana so kyallin fuskarta ya bashi sha'awa babu ruwansa da halinta, ko halayenta. Hasali ba zai shawarci iyayensa ba, sai shi da abokansa su gama komai, sannan sai ya sanar da iyayensa, ba kuma shi da su ba sam sam, sai ya samu yabi takan wani abokin yaɗan yi masa alheri yace ka faɗawa baba na samu aure. in ni na faɗa masa da kaina mita zaiyi ta yi da surutu saboda bai san abinda duniya take ciki ba, Allahu Akbar.
Mai yin haka anya kuwa ƙarshenka zai yi albarka? balle a ce ka tafi ka bar iyayenka ba bu ci babu sha, ba sutura, ba su san ma inda kake ba. Har sai uba ko uwa idan abu yayi tsawo ka ji suna cigiyar ɗansu a rediyo ƙila ɗayansu ne ba lafiya ba ya son ya mutu bai ganshi ba, yana ji ana cigiyarsa a rediyo amma baze komo ba, ya gwammace ya bautawa wasu mutane suna ƙinsa da tare da wukaƙantashi.Harma suna yi masa korar kare amma bai damuba saboda an zare alheri da imani a zuciyarsa don yana saɓawa iyayensa.

FALALAR BIN IYAYE //018//
Mata masu fita yawon bariki suna fita yawan zinace - zinace, kullum iyayensu suna kwana cikin baƙin ciki. Ba sa iya barci kullum daga wajen wannan malami se wajen wannan salihi, suna ta neman addu'a, Allah ya komo da ƴarsu gida ta bar yawan karuwanci. Wata ma harse ubanta ko uwarta, ta mutu ba ta sa ni ma ba, to ta yaya wannan za ta gama da duniya lafiya. Ballantana ma yara mata matasa waɗanda Annabi (S.A.W) ya ce: "Lallai su yarda iyayensu su aurar da su ga wanda iyayen suke so. Amma sai kaga yarinya ta cije ita sai wanda takeso, ko iyayen sun so ko ba su so ba. Duk mai yin wannan ta yaya zata gama lafiya? duk abinda me hankali zeyi ya shawarci iyayensa, ya nema suyi masa addu'a, Allah yana karɓar addu'ar da suka yiwa ɗansu, mai kyau ko marar kyau, kuma duk abinda mutum zeyi dole ne ya nemi yardar iyayensa.

FALALAR BIN IYAYE //019//
KOMAI KA YIWA MAHAIFIYA BAZAKA IYA SAKA MATA BA KAFIN KA YI MATA TA RIGAKA.
Dan Umar Allah ya yarda dashi, ya ga wani mutum ya dau mahaifiya tasa a kan wuyansa yana ɗawafi da ita daura da ka'aba sai ya ce da shi; Ya Ɗan Umar, kana ganin na sakawa uwata? sai Ɗan umar yace ko ɗaya baka saka mata ba; sai dai Allah ya bala ladan bisa ƙanƙanin aikinka.
Allahu Akbar kafin ka goya mahaifiyarka sau nawa ta goyaka? kafin ka bata abinci ko abinsha ko tufa sau nawa ta baka? kafin ka fita yawon neman abinci ka kawo wa iyayenka su ci, sau nawa mahaifinka ya bar garinsu? tun kana ciki ya bar gidansa ya tafi neman don ku ci kai da mahaifiyarka, sau nawa babanka ya gamu da wahala wajen auren mahaifiyarka? sau nawa ya ɓata mata ko ta ɓata masa don tarbiyaka?
Kuma kullum iyayenka suna addu'a Allah ya rayaka kai kuwa kana cewa Allah ya rabaka da su lafiya, wato su mutu su barka a nan. Ina tabbatarwa kowanne ɗan kirki harma marar kirki ya sanifa kullum iyaye so suke ƴaƴansu su rayu har su binne su, da wahala ka samu uba ko uwa suna burin mutuwar ƴaƴansu.

FALALAR BIN IYAYE //020//
FITA KO TAFIYA SABODA NEMAWA IYAYE ABINCI JIHADI NE.
Daga Ka'abu ɗan Ujrata Allah ya yarda da shi ya ce; "Wani mutum ya wuce nan gaban Manzon Allah (S.A.W) Sai sahabbai sukaga fatar jikinsa da jin daɗinsa, sai suka ce ya ma'aikin Allah da de ace wannan saboda Allah ne, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da de ace ya kasance ya fita saboda ƴaƴansa ƙanana ya zama saboda Allah ne. In ya kasance ya fita saboda dattawan iyayensa shima saboda Allah ne. In ya kasance fita yayi saboda ya kare kansa shi ma saboda Allah ne. In ya kasance ya fita saboda riya yana cikin hanyar shaiɗan ne.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce Addu'a uku abar amsawa ce babu kokonto a cikinsu (Addu'ar wanda aka zalunta, addu'ar matafiyi da addu'ar iyaye ga ƴaƴansu). Addu'ar iyaye muhimmiya ce don haka kada ayi wasa da ita.

FALALAR BIN IYAYE //021//
YIWA IYAYANKA ADDU'A KA AIKATA ALKHAIRI KA GIRMAMA ABOKANSU.
Idan mutum ya mutu ayyukansa sun yanke sai abu guda uku: sadaka mai gudana, Ilimi wanda ake amfana dashi da ɗan kirki me yiwa iyayensa addu'a. Allahu Akbar! lallai samun ɗan kirki ba ƙaramin alkhairi ba ne. ya kamata iyaye su tsaya tsayin da ka wajen tarbiyyar ƴaƴansu. don samun addu'a ta alheri bayan rasuwarsu.
An karbo daga Abu Hurairata Allah ya ƙara yarda a gare shi yace; Yana ɗaga darajar mamaci bayan mutuwarsa. sai ya ce ya ubangiji mene ne wannan. sai yace dashi "ɗanka ya nema maka gafara". a nan ya zama wajibi kowanne uba ya zama mai fatan alheri ga ƴaƴansa maza da mata, kuma ya zama mai haƙuri da wasu halaye na ƴaƴan tare da yi musu addu'a Allah ya shiryesu. Haka ma bayan mutuwar mahaifa akwai biyayya gare su muhimmiya.
Maliku ɗan Rabi'a Assa'edi Allah ya ƙara yarda yace ina zaune nan ga Manzon Allah (S.A.W) sai wani mutum daga mutanen Madina ya zakke masa. yace ya Manzon Allah shin akwai wani abu da yayi saura a kaina daga bin iyayena, bayan mutuwarsu? sai Manzon Allah yace, akwai abu huɗu; Yin addu'a a gare su, da neman gafara a garesu, da cika alƙawarin da sukayi da girmama aminansu da sadar da zumunta (wadda baka da wata zumunta sai ta wajensu) wannan shine yayi saura gare ka daga binsu bayan mutuwarsu.

FALALAR BIN IYAYE //022//
Abdullahi ɗan Khaɗɗabi, Allah ya ƙara masa yarda ana buga mana misali mai kyau cikin ɗan kirki. Abdullahi ɗan Dinar yana cewa, haƙiƙa Abdullahi ɗan Umar ya gamu da wani mutum a hanyarsa ta makka. Sai yayi masa sallama, kuma ya ɗauke shi a jakinsa, wanda shi Abdullahi yake hawa, kuma ya bashi rawani wanda yake kansa, sai ɗan Dinar yace, sai muka ce dashi, Allah ya kyautata al'amuranka, waɗannan mutanen ƙauye ne ƙanƙanin abu ma yana isarsu. Sai Abdullahi ɗan Umar yace mahaifin wannan yaron ya kasance; masoyi ne ga Umar ɗan Khaddabi kuma naji Manzon Allah (S.A.W) yace, haƙiƙa muhimmin abinda mutum zeyi bayan mahaifinsa, sadar da zumunta wajen masoyan babansa.
A nan mai hankali zai ga cewa lallai kyautata wa abokan iyaye tare da faranta musu rai abu ne da shari'a ta wajabta shi. Ko da bayan iyayen sun bar duniya kamata ya yi ga kowane ɗan kirki ya dinga ziyartar abokan iyayensa, yana kyautata musu yana shawara da su. Sai fa in ya ga alamar ba za su sa shi a hanyar kirki ba, to a nan yana iya ƙauracewa sai dai ziyara kawai. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya yarda dashi, yace; daga Ma'aiki mai tsira da Amincin Allah ya ce, ka kiyaye ƙaunar babanka kada ka yanke ta, sai Allah ya buɗe haskenka.

FALALAR BIN IYAYE //023//
KYAUTATAWA IYAYE KO BA MUSULMI BANE KAYI SADAKA GARESU SANNAN KAYI MUSU BIYAIYA.
Buraidata, Allah ya yarda da shi ya ce, muna zaune wajen Manzon Allah (S.A.W) , sai wata mata tazo ta ce ta yi sadaka da kuyanga, ga mahifiyarta, amma mahaifiyar ta mutu, sai Manzon Allah ya ce, ladanki ya wajaba. Sai ta ce ya Manzon Allah akwai azumi na wata a kanta, ko na yi mata azumin? sai ya ce ki yi mata, azumin. Sai ya ce kuma batayi hajji ba sam sam, ko na yi mata hajji?. Wannan ya bayyana a gare mu cewa ana biyayya ga iyaye bayan sun bar duniya, kuma a kyautata musu a yi musu addu'a a yi musu hajji, a biya musu bashi.
Wannan wata rahama ce babba daga Allah (S.W.T) wadda ya yi wa bayinsa, waɗanda kuma suka cuci kansu suka taƙaita wajen biyayyar iyaye; amma daga baya su ka ga ne su ka himmatu wajen kyauyatawa iyayensusuna da rai ko basu da rai.Allahu Akbar wannan dama ce wadda Allah (S.W.T) ya yi wq bayinsa don ya gafarta musu.
Akwai wata biyayya wadda ya kamata a kiyaye da ita, wato biyyayyar ƙanwar uwa ko ƴar uwa bayan rasuwar Uwa. Yana nuna wa wanna hadisin: Ɗan Umar ya ce wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ni nayi wani laifi babba ko akwai tuba? sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa kana da Uwa, sai ya ce babu sai ya ce to kanada ƙanwar Uwa? sai ya ce akwai. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa kayi biyayya a gareta.

FALALAR BIN IYAYE //024//
KYAUTATAWA IYAYE KO BA MUSULMI BANE
Akwai halaye kyawawa da ake so ɗa ya yi biyyayya ga iyayensa ko da kafirai ne, wa to ya kyautata musu, ya yi musu hiɗima iyakar ƙarfinsa ta kowanne hali, sai fa in sun nemi ya saɓawa Allah (S.W.T). To anan yana iya saɓa musu kai tsaye, amma kadda ya bisu da baƙar magana. Akwai wani bawan Allah sahabin Annabi (S.A.W) mai suna Sa'ad ɗan Abi Waƙas Allah ya ƙara masa yarda wanda Allah (S.W.T) ya sauƙar da aya cikin Suratul Ankabut a dalilinsa.
Daga Asma'u ƴar Abubakar Allah ya yarda da su ta ce; Mahaifiya ta ta zo gareni amma ba ta musulunta ba a zamanin Annabi (S.A.W), sai na tambayi Annabi na ce masa ya ma'aikin Allah, mahaifiyata ta zo gareni tana da buƙata, ko na sadar ma ta da abinda takeso? sai ma'aiki yace ki sadar da abinda take so (kiyi mata alheri) Ɗan Uwaynata yace kamar yadda yazo a ruwayar Buhari. Allah ya sauƙar a cikinsu Ubangiji bai hanaka ga waɗannan mutane da basu yaƙe ku ba a cikin addini ba su fitar da ku daga gidajenku ba, kuyi musu sassauci, kuyi adalci a garesu, ubangiji yana son ma su adalci. Buhari ya rawaito da Muslim da Abu Dawud da Baihaƙi.

FALALAR BIN IYAYE //025//
BIYAYYA GA UWA.
Bin Uwa muhimmin abu ne, wanda Allah (S.W.T) ya wajabta shi a kan kowane mumini.
Daga Abu Hurairata, Allah ya yarda dashi yace, wani mutum ya zo zuwa ga Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce, ya Manzon Allah wane ne mafi cancanta da kyautatawa daga gare ni? sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi Mahaifiyarka, sai ya ce sannan kuma wa? sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce mahaifiyarka, sai ya ce sannan kuma wa? sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce Mahaifiyarka, sai ya ce sannan kuma wa? sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce mahaifinka.
Daga Bahzu bin Hakim, daga babansa daga kakansa ya ce, ya Manzon Allah (S.A.W) wa zan bi? Ya ce mahaifiyarka,
Na ce wa zan bi? ya ce mahaifiyarka,
Na ce wa zan bi? ya ce mahaifiyarka,
Na ce wa zan bi? ya ce mahaifiyarka.
Sannan na kusa sannan na kusa. waɗannan hadisai suna nuna mana cancantar uwa akan komai, wajen biyayya sadarwa, hidima saboda irin wahalar da tasha fama kafin haihuwarka, da bayan haihuwarka. Shi ya sa shari'a ta ƙeɓanci uwa, da riɓi uku wanda uba bai samu ba, sai rabo ɗaya tak. wannan yana ƙara nuna mana muhimmancin girmama mahaifiya a kan mahaifi.

FALALAR BIN IYAYE //027//
KAFIN KA ƊAUKI MAHAIFIYARKA ITACE TA FARA ƊAUKANKA A CIKI A HANNU A BAYA.
Daga Buraidata, haka wani mutum ya zo ga Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce ya Manzon Allah, ni na ɗauki mahaifiyata akan wuyana, farsahi biyu cikin rairayi mai tsanin zafi, da za'a jefa tsokar nama cikinsa da ya gasa shi, ko na sakamata? Sai Annabi (S.A.W) ya ce mai yiwuwa ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da ta yi maka. Hasnul Basri ya ce wato haƙƙin uba shi ne mafi girma, bin uwa shi yafi ƙarfi.
Daga Sulaimana ɗan Buraidata, daga babansa, cewa haƙiƙa wani mutum ya kansance cikin ɗawafi ɗauke da mahaifiyarsa, yana ɗawafi da ita, sai ya tambayi Manzon Allah (S.A.W) shin na biya haƙƙinta? sai Manzon Allah ya ce, sam-sam ko da ƙwarzane ɗaya. Wannan yana nuna wahalar da uwa take sha, ko ta sha a kan ɗanta. Yaya za'ayi ya saka mata, wahalar ɗaukar ciki, sai ta haihuwa, sai ta shayarwa, sai ta reno da tarbiya.
Yaya za'ayi yanzu a samu saurayi da ze iya ɗaukar mahaifiyarsa a cikin zafin rairayi bai yi tunanin shan wahala ba? mafiya yawan yaran yanzu ma a mota suke ɗaukar iyayensu, amma har ƙosawa suke yi in har idan iyayen sun yi ɗan jinkiri ba su fito ba. mahaifiyarka ta kasance ta na fatan rayuwarka, kai kuwa kana yi mata fatan rabuwa da ita. Uwa kullum cikin hiɗimar ɗanta take, ba ya girma a wajenta kuma bata ƙosawa da yi masa hidima da sake sabon reno, da sabuwar tarbiyya har ta koma ga Allah.